• Dalilan Da Suka Sa Ake Gudanar Da ‘’Boxing Day’’ A Ranar 26 Ga Disamba
    Dec 26 2024

    Send us a text

    Ranar 26 ga watan disambar duk shekara ne ake rabon kyaututtuka a cigaba da gudanar da bukuwan kirsimeti wanda ake ma wannan rana da boxing day.

    Alumma da dama da sunji boxing day abun dake fara zuwa musu a rai shine wasan dambe da ake yi a wasu kasashe da ake kira da boxing.

    Shirin Najeriya A Yau zai yi duba ne kan wannan rana na Boxing Day don warware zare da abawa.

    Show More Show Less
    25 mins
  • Abin Da Ya Sa ’Yan Sanda Suke Kama Mutanen Da Ba Su Ji Ba, Ba Su Gani Ba
    Dec 24 2024

    Send us a text

    Lokacin bukukuwa lokaci ne da ake samun karuwar zirga-zirga da hada-hadar jama’a.

    Wannan ne ya sa hukumomin da nauyin samar da tsaro ya rataya a wuyansu suke kara kaimi wajen ganin sun tabbatar da doka da oda.

    Sai dai wasu ’yan Najeriya sukan yi zargin cewa ’yan sanda kan yi amfani da wannan dama don kamen mutane babu gaira babu dalili.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi duba ne kan sahihancin wannan zargi.

    Show More Show Less
    27 mins
  • Abubuwan Da Suke Haddasa Turmutsutsu A Najeriya
    Dec 23 2024

    Send us a text

    Lokacin da Victoria Faith, wata baiwar Allah mai shekara 27 da haihuwa, ta je coci a Gundumar Maitama da ke birnin Abuja, cike take da kyakkyawan fatan samo abincin da za ta yi bikin Kirsimeti da shi.

    Amma a maimakon haka da kyar ta tsira da ranta, ta yi “sa’a” da ta farka a gadon asibiti, bayan da aka tattake ta a turmutsutsun da ya yi sanadin mutuwar mutum 10.

    Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai saurari yadda Victoria ta ji, sannan ya yi nazari a kana bin da yake haddasa turmutsutsu a tasakanin ’yan Najeriya, da ma hanyoyin hana shi aukuwa.

    Show More Show Less
    26 mins
  • Yadda Direbobi Suke Zaman Kashe Wando A Tasha
    Dec 20 2024

    Send us a text

    A shekarun baya, idan mutum ya shiga tashoshin mota a biranen Najeriya a irin wannan lokaci, zai same su cike da jama’a da hayaniya.

    Sai dai a bana, a tashoshi da dama, wasu direbobin a kwance suke yayin da fasinjoji suke zaune tsawon sa’o’i suna jiran tsammanin motoci su cika.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan faruwar hakan a karshen wannan shekarar.

    Show More Show Less
    27 mins
  • Hadarin Da Ke Tattare Da Aiwatar Da Kasafin Kudi Biyu A Lokaci Guda
    Dec 19 2024

    Send us a text

    Yayin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yake gabatar da Kudurin Kasafin Kudi na 2025, shi kuwa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio dauke hankalin jama’a ya yi da sanar da tsawaita wa’adin Kasafi na bana zuwa tsakiyar badi.

    Sai dai masana sun yi gargadin cewa wannan lamari ka iya haifar da rikita-rikita a bangaren tattalin arziki da ma wasu bangarorin.

    Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda aiwatar da Kasafin Kudin bara da na bana a lokacin guda zai shafi rayuwar ’yan Najeriya.

    Show More Show Less
    20 mins
  • Yadda Tamowa Ke Yaduwa Kamar Wutar Daji a Katsina
    Dec 17 2024

    Send us a text

    Wani rahoto da Kungiyar Likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta fitar ya nuna cewa Arewa maso Yamma ta fi kowacce shiyya yawan karuwar yara masu tamowa.

    A shiyyar kuma, inji rahoton, Katsina ta fi ko wacce jiha yawan masu fama da cutar.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi bincike ne don gano yadda lamarin yake.

    Show More Show Less
    24 mins
  • Rayuwar Maza Masu Fama Da Matsalar Rashin Haihuwa
    Dec 16 2024

    Send us a text

    Rashin haihuwa matsala ce da ke wargaza gidajen aure da dama a wannan zamani.

    Da an samu shekara biyu zuwa uku bayan an daura aure ba tare da an samu karuwa ba za a fara yamadidi da matar a kan ba ta haihuwa.

    Sai dai Likitoci sun ce maza ma ka iya fama da wannan larura saboda wasu dalilai.
    Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne a kan wadannan matsalolin da suke hana maza haihuwa.

    Show More Show Less
    22 mins
  • Yadda Ya Kamata Alaka Ta Kasance Tsakanin 'Yan Sanda Da Al'umma
    Dec 13 2024

    Send us a text

    Babban alhakin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya dora wa rundunar Yan Sanda shi ne kare rayuka da dukiyoyin yan kasa.

    Sai dai a lokuta da dama, akan samu fito-na-fito da 'yan kasa ke yi da 'yan sandan sakamakon zargin wuce gona da iri wajen gudanar da aiyyukan nasu.

    Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan yadda ya kamata alaka ta kasance tsakanin jami'an 'yan sanda da al'ummar kasa.

    Show More Show Less
    27 mins